News
Aƙalla mutum 2,700 aka tabbatar sun rasu a girgizar ƙasar Turkiyya da Syria
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Adadin waɗanda suka rasu a Turkiyya sakamakon girgizar ƙasar da aka yi a ƙasar ya ƙaru zuwa 1,762 kamar yadda hukumar kare afkuwar bala’i ta ƙasar ta bayyana.
Idan aka haɗa jumulla daga girgizar ƙasa ta farko da aka yi da asuba da wadda aka yi da hantsi a Turkiyya da Syria sun haura 2,700 bayan rahotanni daga Syria sun bayyana cewa mutum 1,000 suka rasu.
Advertisements
