News
Aƙalla mutum 2,300 aka tabbatar sun rasu a Turkiyya da Syria
DAGA ABDULRASHEED MUHAMMAD RABIU
Adadin mutanen da suka rasu a Turkiyya ya ƙaru sakamakon girgizar ƙasar da aka yi a yau inda adadin ya kai 1,498, kamaryadda hukumar kare afkuwar bala’i ta ƙasar ta bayyana.
Idan aka haɗa jumulla da na girgizar ƙasar da aka yi da asubahi da kuma wadda aka yi da hantsi adadin ya kai 2,300, bayan an sake tabbatar da mutuwar mutum 810 a Syria, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana.
Ƙasashe da dama a faɗin duniya dai suna ta jajantawa ƙasashen Turkiyya da Syria tare da yi musu tayin bayar da agaji.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
