Connect with us

News

An gurfanar da jami’in gidan yari kan zargin sayar da aiki

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta ta gurfanar da wani jami’in tsaron gida yari mai suna mista Eyimoga Moses a gaban Babbar Kotun Tarayya a Makurdi, babban birnin jihar Benue, inda take zarginsa da sayar da aiki.

ICPC tqa ce tana zargin Moses wanda ke aiki a gidan yari da ke jihar Nasarawa da laifin karɓar 800,000 daga hannun wasu ma’aurata da karyar cewa zai sama musu aiki a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Lafia.

Masu Gine Gine A Filayen Gwamnati, Muna Basu Shawara Da Su Dakata Daga Yau – Abba 

Sai dai Moses ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi, inda aa bayar da belinsa yayin da ake ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali a Makurdi har sai ya cika sharuɗan belinsa da aka bayar.

Advertisement

An ɗage zaman kotun har sai 20 ga watan Yunin 2023 domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending