Connect with us

News

Masu Gine Gine A Filayen Gwamnati, Muna Basu Shawara Da Su Dakata Daga Yau – Abba 

Published

on

 

 

Advertisement

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya shawarci dukkanin masu gine gine a filayen gwamnati da su dakata nan take.

 

Advertisement

Abba Kabir Yusuf ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ta bakin sakataren yada labaran sa Sunusi Bature Dawakin Tofa.

Zargin Kafa Gwamnatin Riƙo A Najeriya Abin Fargaba Ne – Jam’iyyu.

Abba ya ce yana shawartar dukkan wasu mutane, kungiyoyi ko kamfanoni da suke gine gine a filayen gwamnati kama daga asibitoci, makarantu, kasuwanni, makabartu da ma dukkan wani wuri da aka san na gwamnati ne, da su dakatar da ginin nan daga yau ɗinnan har sai sabuwar gwamnati wadda zata shigo daga 29 ga watan Mayu ta kama aiki sannan ta san me zata yi akan lamarin.

Advertisement

 

Zabbaben gwamnan ya ce shawara ce yake basu, wanda duk bai dauki shawara ba, toh ya zargi kan sa da abinda ka iya biyo baya da zaran lokacin da gwamnati mai shigowa ta zo zata dauki mataki.

Advertisement

 

Abba Kabir Yusuf ya sha zargin gwamnati Abdullahi Umar Ganduje mai barin gado da cewa tana sayar da filayen gwamnati ana yin gine gine ba bisa ka’ida ba.

Advertisement

 

Izuwa wannan lokaci dai ba a ji martanin gwamnati mai barin gado ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending