Connect with us

News

Zargin Kafa Gwamnatin Riƙo A Najeriya Abin Fargaba Ne – Jam’iyyu.

Published

on

 

Kwamitin tuntuɓa tsakanin jam’iyyun Najeriya ya ce zargin kafa gwamntin riƙo a ƙasar, babban abin tayar da hankali ne da cusa fargaba.

Advertisement

Shugaban kwamitin, Engr Yabagi Sani ya ce “Ba ma mu ‘yan siyasa ba kaɗai ba, duk wanda ke kishin Najeriya, yake da kishin ci gaban Najeriya, yake kishin dimokraɗiyya ta kafu a Najeriya.

Ƴan Sanda Sun Kama ɓarayin Babura Da ƴan Fashin Waya A Kano

Idan aka dubi matsayin Najeriya ba ma a Afirka kaɗai ba, a duniya gaba ɗaya, abin da DSS ta fito da shi, abu ne na fargaba”.

Advertisement

Engr. Sani na mayar da martani ne kan zargin da DSS ta yi cewar wasu jiga-jigan ‘yan siyasa a ƙasar na shirya maƙarƙashiyar kafa gwamnatin riƙon ƙwarya don hana rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasa nan gaba cikin wata Mayu.

Ya ce a ganinsa, abin da ya janyo kitsa irin wannan maƙarƙashiya da ake zargi, shi ne rashin gamsuwar da mai yiwuwa wasu ‘yan siyasa ke da ita kan zaɓukan 2023 da kammala a baya-bayan nan.

Advertisement

“Lallai waɗanda ba su gamsu da abin da hukumar zaɓe ta fito da shi ba ne, mai yiwuwa cikinsu ne aka samu waɗanda ke nuna fushinsu,” in ji Engr Sani.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending