Connect with us

News

Wani soja ya fallasa takardun sirrin Amurka

Published

on

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana fallasar a matsayin babbar barazana ga tsaron kasar, inda takardun ke nuna yadda Amurka ke cikin dari-dari dangane da yakin Ukraine da kuma wasu bayanan sirri da suka shafi kasashen duniya hatta wadanda ke hulda da ita.

Shan Shisha Zai Iya Haifar Da Ciwon Zuciya —Bincike

Takardun sun nuna cewa, Amurka ta yi wa kawayenta wato Isra’ila da Korea ta Kudu leken asiri .

Advertisement

Wadandan takardun sun shafe tsawon makwanni suna yawo a dandalin sada zumunta na Discord, amma ba su haddasa tayar da jijiyoyin wuya ba har sai da kafafen yada labarai suka wallafa su a kwanan nan.

Masu kula da dandalin na Discord sun shaida wa Jaridar Washington Post cewa, wani mutun ne ya wallafa daruruwan shafukan takardun bayan ya shaida musu cewa, shi ma’aikaci ne a wani sansanin sojin Amurka.

Advertisement

Bayanai na cewa, wadandan takardun sun kunshi bayanai masu tsantseni, inda har wasu daga cikinsu aka sanya musu alamar “NOFORN” ma’ana kar a kuskura a yi musyar su da ‘yan kasashen ketare.

Tuni jami’an Binciken Manyan Laifuka na Amurka, FBI suka cafke mutumin da ake zargi da fallasa takardun sirrin kasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending