News
An Yankewa Wani Tela Hukuncin Daurin Shekaru Uku A Gidan Yari
Wata kotun majistare dake jihar Ondo ta yankewa wani tela mai shekaru 41, Tajudeen Olajide, hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bisa samunsa da laifin cin zarafin wani mutum mai suna Olamiposi Oluwatobi,kamar yanda jaridar Daily Post ta rawaito
Wanda aka yankewa hukuncin da aka samu da aikata laifuka guda daya na cin zarafi ana zarginsa da bugawa Oluwatobi makulli a idon sa.
A cewar mai gabatar da kara, Sulaiman Abdulateef, lamarin da ya faru a ranar 10 ga watan Disambar shekarar 2021, a cikin sashin asibitin Crown da ke Akure, babban birnin jihar, ya yi sanadin cutar da wanda abin ya shafa.
Dan sanda mai gabatar da kara ya kara bayyanawa kotun cewa Olajide ya aikata laifin ne a lokacin da suka baiwa hammata iska akan titi.
Abdulateef ya kara da cewa wanda abin ya shafa ya samu rauni a idon sa wanda ya yi sanadin makanta gaba daya.
Sai dai wanda ake tuhumar ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Alkalin kotun, Tope Aladejana, ya same shi da aikata laifin, inda daga bisani ya yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari tare da zabin biyan diyya na naira N700,000 ga wanda abin ya shafa.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
