Connect with us

News

Ranar ‘Yancin ‘Yan Jaridu: Lawan Ya Jinjinawa ‘Yan Jaridun Nigeria

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, a ranar Larabar nan, ya yaba wa ‘yan jaridun Najeriya a ranar bikin ‘yancin ‘yan jarida ta duniya.

 

Advertisement

Lawan a wata sanarwa da ya fitar ranar Larabar a Abuja ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mista Ola Awoniyi, ya ce ‘yan jarida sun ba da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban zamantakewa da siyasa da tattalin arzikin Najeriya.

Majalisar Wakilai Ta Hana Gwamnatin Taraiyya Cefanar Da Kanfanin Sarrafa Karafa na Ajaokuta

“’Yan jaridan Najeriya sun cancanci a yaba musu saboda gudunmawar da suke bayarwa ga dimokuradiyya da gudanar da mulki gaba daya a Najeriya a matsayin kasa ta samu hudin kai.

Advertisement

 

“Kaddamar da ‘yancin aikin jarida ba wai kawai kare hakkin wani muhimmin bangare ne na al’umma ba, yana kuma inganta ‘yancin fadin albarkacin baki da ra’ayi.

Advertisement

 

“A bisa haka ne Majalisa ta tara ta tabbatar a cikin shekaru hudun da suka gabata cewa babu wata doka da ke karkashinta da ke cin zarafin wadannan hakkoki,” in ji Lawan.

Advertisement

 

Ya yi wa ‘yan jarida fatan alheri.

Advertisement

 

Kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN ya bayar da rahoton cewa, Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana ranar 3 ga watan Mayu a matsayin ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya.

Advertisement

 

Ana yin bikin ne kowace shekara don gane irin namijin kokarin da kuma gudunmawar da ‘yan jarida ke bayarwa wajen gano zurfafan gaskiyar al’umma da ba a san su ba.

Advertisement

 

Jaridar Punch ta rawaito cewa Taken ranar ‘yan jarida ta duniya ta 2023 ita ce ‘Sanya makomar ‘yancin kai: ‘yancin fadin albarkacin baki a matsayin ragowar hakkokin bil’adama.

Advertisement

 

A cewar UNESCO, “Wannan shekara ce ta 30 da Majalisar Dinkin Duniya ta yanke shawarar ayyana ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya.” (NAN)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending