Connect with us

News

Majalisar Wakilai Ta Hana Gwamnatin Taraiyya Cefanar Da Kanfanin Sarrafa Karafa na Ajaokuta

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

A ranar Litinin ne, Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirin ta na cefanar da kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta da kamfanin hakar ma’adinai na kasa domin tuntubar masu ruwa da tsaki.

 

Advertisement

Majalisar ta amince da kudirin da Abdullahi Ibrahim Halims ya gabatar inda ta gayyaci ministan ma’adinai da karafa domin ya yi mata cikakken bayani kan shirin cefanar da kanfanonin biyu.

Ma’aikatan Sufurin Jiragen Sama Sun Janye Aniyarsu Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani. 

Dan majalisar ya baiyana shirin cefanar da kanfanonin da tsakar rana, yayin da ya ragewa gwamnati mai ci kasa da kwanaki 30 wa’adinta ya kare, bai dace ba kuma rashin kishin kasa ne.

Advertisement

 

Ya yi kira da a samar da wasu tsauraran sharudda koda za’a aiwatar da tsarin ba wai yinshi sake babu kaidi ba.

Advertisement

 

Daga karshe majalisar wakilan ta umarci kwamitinta mai kula da bangaren ma’adinai da ya yi gaggawar bincike kan lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending