News
Majalisar dokokin Kano ta amince da mutanen da ta tattance don nada su kwamishinoni
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Majalisar dokokin Kano ta amince da mutanen da ta tattance don nada su kwamishinoni
A ranar Talata ne gwamnan Kano ya aikewa majalisar sunayen mutane 19 da yake so majalisar ta tantance don nada su kwamishinoni.
Inda a ranar Laraba majalisar ta tantance mutane 16 tare da amincewa dasu a Alhamis din nan.
Muhuyi ya sha alwashin bincikar Ganduje game da bidiyon dollar
Cikin mutane 19 dai akwai mutum biyu da suka tafi aikin hajji wanda hakan yasa ba a tantance su ba sai kuma mataimakin gwamnan Kano wanda aka amince dashi ba tare da ya halarci tantamcewar ba.
Shugaban masu rinjaye dan majalisa mai wakiltar Dala Lawal Hussain yayiwa wakilin mu na majalisa Aminu Abdullahi Ibrahim karin bayani.
Majalisa ta kuma kafa kwamiti da zai jagoranci fitar da kwamitocin majalisar na bangarori daban daban wanda shugaban majalisar zai jagoranci kwamitin.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
