News
Shin Da Gaske An Bude Bodar Legas Don Shigo Da Motoci?
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Labarai da ke yawo a kafafen sada zumunta a Najeriya suna ta bayyana cewa Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin a bude bodar kasar.
Tun a ranar Laraba aka fara yada labaran, amma daga Alhamis sai labarin ya fara canjawa, inda aka ware cewa wai bodar Seme ta Jihar Legas kawai aka bude domin a rika shigo da motoci.
Majalisar dokokin Kano ta amince da mutanen da ta tattance don nada su kwamishinoni
Daily trust ta bi diddigin labarin domin gano ainihin inda aka samo rahoton, amma hakar ta bai cim ma ruwa ba domin babu wata babbar kafar watsa labarai da ta rawaito labarin.
Sai dai a wani labarin da Jaridar Punch ta ruwaito, ta rawaito Daraktan Sufuri na Kasa na Ma’aikatar Sufuri, Ibrahim Musa yana cewa a zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari masu fito suka rubuta wasika zuwa ga Ministar Sufuri inda suka bukaci a bude bodar.
A cewar shi, “Mun taba zuwa nan (Bodar Seme) da tsohon Minista a Ma’aikatar Sufuri inda masu fito suka bukaci a bude bodar domin cigaba da shigo da motoci. Da kuma koma ministan ya umarce mu da mu shirya takardar da zai gabatar a gaban Majalisar Zartarwa, wanda kuma hakan aka yi. Sannan bayan ya gabatar an amince da bukatar,” in ji shi, sannan ya kara da cewa bayan an amince da bukatar, sai majalisar ta amince a bar batun a gadar da shi zuwa ga sabuwar gwamnati domin ta yanke hukunci.
Da wannan bayanin ne Jaridar Punch ta kafa hujja, inda ta rawaito cewa an kusa bude bodar, amma a cikin labarin baki daya, babu inda ta ce Gwamnatin Tarayya ta ce a bude bodar ta Seme.
Aminiya ta tuntunci wani jami’in Hukumar Kwastam, inda ya tabbatar da cewa labarin na kanzon kurege ne.
Bisa dalilan binciken jaridar indaranka, wannan labarin na bude bodar Seme domin shigo da motoci ba gaskiya ba ne. Amma ta yiwu a waiwayi lamarin kasancewar daraktan ya ce sun gabatar da shi a baya duk da cewa hakan yana ta’allaka ne da tsarin sabuwar gwamnatin da sabon minista da za a tura Ma’aikatar Sufuri.
