Connect with us

News

An Kama Dan Shekara 23 Da Kunshi 605 Na Tabar Wiwi A Jahar Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

An cafke wani matashi mai shekara 23 dauke da kunshi 605 na tabar wiwi a unguwar Kofar Mata da ke Karamar Hukumar Birni ta Jihar Kano.

Advertisement

 

’Yan sanda sun ce sun cafke matashin ne da buhuna makare da tabar wiwi, bayan mazauna unguwar Kofar Mata sun kai korafi cewa dilolin miyagun kwaya sun addabi unguwar.

Advertisement

 

Wani mutum Ya Yi Dambe Da ’Yan Bindiga Ya Kwaci Mahaifinsa A Kano

“Bayan samun korafi daga mazauna unguwannin Kofar Mata da Mandawri game da wani dilan miyagun kwayoi da ke sayar wa matasan unguwannin, Kwamishinan Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Muhammed Usaini Gumel ya ba da umarni aka kamo wanda ake zargin a unguwar Kofar Mata.

Advertisement

 

“Amma wanda ake zargin dan asalin unguwar Rijiyar Lemo da ke Karamar Hukumar Dala ne, kuma shekarunsa 23

Advertisement

 

“A yayin bincike an gano kunshi 605 na ganyen da ake zaton tabar wiwi ce ” in ji sanarwar da rundunar ta fitar.

Advertisement

 

Da yake gabatar da wanda ake zargin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Muhammed Usaini Gumel ya ce matashin ya yi ikirarin cewa shi sana’ar gwangwan yake yi a Legas, da zai zo Kano ne wani abokinsa ya ba shi sakon ya kawo masa gida.

Advertisement

 

Matashin ya ce, “Na zo gida ne daurin aure daga Legas; Da zan zo ne wani abokina ya ba ni sakon wadannan buhunan in kawo masa gida.”

Advertisement

 

A cewarsa, “Ni ban san cewa wiwi ba ce a ciki, saboda a rayuwa ta ban taba sha ba — ko sanin ta ban yi ba.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending