Connect with us

News

Hukumar NSCDC ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin barayin shanu ne a jihar Jigawa.

Published

on

NSCDC

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Hukumar tsaron farin kaya ta kasa NSCDC ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin barayin shanu ne a jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, CSC Adamu Shehu, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya raba wa manema labari.

Advertisement

Majalisa Dattawa ta amince da naɗin mutum 45 a matsayin ministocin Tinubu.

Ya ce an kama wadanda ake zargin, Abdullahi Buba na Garin Dole, karamar hukumar Itas/Gadau, jihar Bauchi, da kuma Alhaji Jubril na Bursari, karamar hukumar Dapchi, jihar Yobe, a ranar Asabar da karfe 1 na safe a karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa.

Ya bayyana cewa maigidan ne ya kama wadanda ake zargin, inda suka yi taka-tsan-tsan a cikin dare da nufin kamo barawon da a baya ya sace shanu a unguwar.

Advertisement

 

An sace masa shanu hudu, biyu kuma na makwabcinsa, Alhaji Hardo, wadanda kudinsu ya haura N2,000,000.

Advertisement

Jaridar Daily post ta rawaito cewa Shehu ya ce bincike ya nuna cewa Abdullahi tare da ‘yan bindigar na satar shanu ne a tsakanin karamar hukumar Kiyawa da ke Jigawa da kuma garin Azare a Bauchi.

Ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifin satar shanu tare da kai su jihar Kano.

Advertisement

Kakakin hukumar NSCDC ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bisa laifukan hada baki, yin kutse, da niyyar yin sata, da kuma sata bayan bincike.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending