News
Bai Kamata A Raba Mana Tallafin Kudi Daidai Da Sauran Jahohi Ba-Gwamnatin Jahar Kano
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake duba tsarin rabon kudi na Palliatives Allocation domin karin kaso ga jihar Kano kasan cewar ta jihar da ta fi kowacce yawan al’umma a kasar nan.
Gwamnan jihar Alh Abba Kabir Yusuf ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen taron majalisar zartarwa na mako-mako a dakin taro na gidan gwamnatin Kano.
Indaranka:Yadda Ɗan shekara 94 ya yi wa Ƴar shekara 13 fyade
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta damu matuka da halin kuncin da al’ummar jihar ke ciki sakamakon illar cire tallafin. Yayin da ya ke yaba wa kokarin da gwamnatin tarayya ta yi na samar da abinci, gwamnan ya yi kira da a ware wani Jason ga Kano saboda yawan al’ummar jihar.
A cewar Gwamna Abba a cikin kokarinmu na taimaka wa jama’a a jihar ta fuskar rage tallafin da ake samu, mun sayi hatsi na Naira biliyan 1.6 daga Gwamnatin Tarayya wanda ya hada da gero da masara da shinkafa da dai sauransu.
Gwamnan ya kara da cewa wannan kari ne a kan tirelolin shinkafa guda biyar da gwamnatin tarayya ta baiwa jihar inda ya tabbatar da cewa an riga an tsara hanyoyin da za a bi domin ganin sun isa ga marasa galihu a cikin al’umma.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar na shirin samar da wani shiri na samar da Shanu, Tumaki da Akuya nan ba da jimawa ba domin karfafawa mata musamman wadanda ke yankunan karkara domin dogaro da kai da kuma habaka tattalin arziki.