News
Ku Magance Cutar Dake Haifar Da Juyin Mulki Ba Alamomin Cutar Ba – Atiku Ya Aika Sako Ga Shugabannin Afirka
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, a zaben shugaban kasa na 2023, Atiku Abubakar ya yi kira ga shugabannin Afirka da su mayar da hankali kan abubuwan da suka haifar da karuwar juyin mulkin baya-bayan nan a fadin Nahiyar, maimakon bibiyar alamomin juyin mulkin.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa ta dandalin sada zumunta na X da wanda aka fi sani da Twitter a baya, inda yake mayar da martani kan juyin mulkin da aka yi a kasar Gabon, wanda shi ne na takwas a nahiyar Afirka tun shekarar 2020.
Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Wasu Ayyuka 2 Da Buhari Ya Fara
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce juyin mulkin da aka yi a kasar dake Afirka ta Tsakiya abun dabawa ne, yana mai cewa kamata ya yi ayi duk mai yiwuwa don dorewar dimokuradiyya a nahiyar.
Sai dai ya dage cewa shugabannin Afirka su yi maganin cutar da ke haifar da juyin mulki ba alamun cutar