Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Wasu Ayyuka 2 Da Buhari Ya Fara

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta hannun Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bada umurnin dakatar da sallama filin tashin jiragen sama da kamfanin jirgin sama na kasa.

Advertisement

Sallama filin tashin jiragen saman da jirgin sama na kasa na cikin manyan ayyukan da tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi a bangaren sufurin jiragen sama.

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 5 a jahar Adamawa

Amma, Keyamo, yayin wata ziyara da ya kai filin Tashi da Saukan Jirage Na Murtala Mohammed (MMIA) da ke Legas a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, ya ce a dakatar da ayyukan har zuwa wani lokaci nan gaba.

Idan za a iya tunawa an amince da yin ayyukan ne a kusan karshen wa’adin gwamnatin Shugaba Buhari, kuma hakan ya janyo cece-kuce tsakanin masu ruwa da tsaki.

Advertisement

Gwamnatin Tarayyar ta sanar da sallamar da filin tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja da Murtala Mohammed da ke Legas (MMIA) kimanin mako guda kafin karewar wa’adin gwamnatin Shugaba Buhari.

James Odaudu, mataimaki na musamman ga tsohon Ministan Sufuri, Hadi Sirika na wancan lokacin, ya bayyana amincewa da sallamar da su a taron FEC.

Tsohon ministan ya bayyana cewa kamfanin ‘Corporation American Airport Consortium ne wanda za a sallamarwa kadarorin, ya kunshi Corporation American Airports, Mota Engil Africa, and Mota Engil Nigeria.

Advertisement

An rantsar da Keyamo a matsayin minista a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, lokacin da Shugaba Tinubu ya kaddamar da ministocinsa 45.

Shugaba Tinubu ya tura sunayen mutane 48 ga Majalisar Dattawa domin tantancewa amma uku cikinsu ba a tantance su ba.

Ministan ya yi bayani a shafinsa na Twitter inda yace:

Advertisement

“Ba a yanke hukuncin karshe ba kan batun sallamar da jirgin saman kasa da filayen jiragen sama.”

“An dakatar da abin ne don tantance lamarin tare da warware korafe-korafen saboda amfanin yan Najeriya kuma an yi wa Shugaban Kasa bayani.”

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *