News
Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 5 a jahar Adamawa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa, ADSEMA, ta tabbatar da cewa akalla mutane biyar ne ambaliyar ruwa ta tafi da su a sassa daban-daban na jihar Adamawa.
Sakataren zartarwa na hukumar Dr Suleiman Muhammad ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Yola ranar Alhamis.
Muhammad ya ce gidaje da wuraren kasuwanci da dama a kananan hukumomin Fufore, Yola ta Kudu da Mubi ta Kudu ambaliyar ta shafa.
Ya shawarci mazauna yankunan kogunan jihar da su kara taka tsantsan sakamakon rufe madatsar ruwa ta Lagdo a kasar Kamaru.
Kwanan nan hukumar ta gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki, inda ta bukaci al’ummar da ke fama da ambaliyar ruwa da su koma wurare masu aminci a cikin jahar ta Adamawa.
Muhammad ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da gangamin wayar da kan jama’a game da ambaliyar a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.
“An shawarci mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su bi umarnin da kwararru suka bayar. Dole ne su yi taka tsantsan.
Shugaban ADSEMA ya bayyana kudurin hukumar na gudanar da aikinta yadda ya kamata na tafiyar da al’amuran gaggawa a jihar.
