Connect with us

News

Na’urar Bibas Ce Kadai Aka Wajabta Ma Hukumar Zabe INEC Yin Aiki Da Ita – Kotu

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, Ta ce ba dole ba ne Hukumar zabe ta kasa INEC ta rika tura sakamakon zabe kai tsaye ta hanyar amfani da na’ura, Inda ta baiyana cewar Hukumar tana da ‘yancin yin amfani da hanyar da ta yi niyyar yin amfani da ita wajen tura sakamakon zabe.

Kotun ta baiyana cewar, Na’urar tantance masu zabe ta BIBAS ita ce aka wajabtawa hukumar zaben ta kasa yin amfani da ita.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Kara Farashin Mitar Wutar Lantarki

Kazalika kotun ta yi watsi da zargin da Atiku Abubakar da jam’iyyar sa ta PDP suka yi na cewar, Tinubu ba cikakken dan Najeriya ba ne, kuma yana da shaidar zama ta ‘yan kasashe guda biyu.

Haka zalika kotun ta yi fatali da zargin da masu kara suka yin a cewar Tinubu bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ba, saboda zarginsa da aikata lefuka a kasar Amurika.

Advertisement

Wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya Ta Kara Farashin Mitar Wutar Lantarki

Rashin wutar lantarki da ake fama dashi tun kafin yanzu ya kara tsananta jiya a nan Jihar Kano, A yayin da kanfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya tsayar da aiyukansa kacokan, Lamarin da ya haifar da daukewar lantarki baki daya a cikin birnin Kano.

Advertisement

Wata sanarwa da shugaban sashin sadarwar kanfanin, Sani Bala Sani ya fitar, Ya alakanta daukewar wutar lantarkin da yin biyayya ga umarnin kungiyar kwadago ta kasa na tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu.

Sanarwar da aka wallafa a shafin X na kanfanin, Ta baiyana cewar za’a cigaba da fuskantar matsalar daukewar wutar lantarkin, kasancewar yajin aikin gargadin zai ci gaba da kasancewa a yau Laraba.

Advertisement

Shima mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Ado Riruwai, ya tabbatar da cewar kungiyarsu ta rufe dukkanin wasu ofisoshin gwamnati dake jihar Kano, domin tabbatar da yajin aikin gargadin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending