News
Tinubu Ya Yi Maraba Da Hukuncin Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Bayan yanke hukunci da kotun ta yi a daren jiya, Shugaban kasa Bola Tinubu wanda a yanzu haka yake halartar taron kungiyar G20 ta kasashe masu yunkurin habaka tattalin arzikin duniya, ya yi murnar samun nasarar da ya yi a gaban kotun tare da mukarrabansa da suka take masa baya zuwa kasar ta Indiya.
A wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sadarwar zamani, An nuno shuguban kasar ya na kallon yadda take wakana a zaman kotun kai tsaye ta hanyar amfani da Talabijin.
Kanfanonin Kasar Indiya Zasu Zuba Jarin Dala Bilyan 14 A Najeriya
Bayan tabbatar da nasararsa ta lashe zaben shugaban kasa, Dansa Seyi Tinubu da sauran mutanen dake tare dashi, sun ta yashi murnar samun nasara a kotu.
Daga bisani kuma, Shugaban kasar ya fitar da wata sanarwa ta hannun Kakakinsa, Ajuri Ngelale, wanda ya nuna ya yi maraba da yadda hukuncin kotun ya kasance, yana mai yin kira da a hada hannu wuri daya domin gina kasa.
Rashin wutar lantarki da ake fama dashi tun kafin yanzu ya kara tsananta jiya a nan Jihar Kano, A yayin da kanfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya tsayar da aiyukansa kacokan, Lamarin da ya haifar da daukewar lantarki baki daya a cikin birnin Kano.
Wata sanarwa da shugaban sashin sadarwar kanfanin, Sani Bala Sani ya fitar, Ya alakanta daukewar wutar lantarkin da yin biyayya ga umarnin kungiyar kwadago ta kasa na tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu.
Sanarwar da aka wallafa a shafin X na kanfanin, Ta baiyana cewar za’a cigaba da fuskantar matsalar daukewar wutar lantarkin, kasancewar yajin aikin gargadin zai ci gaba da kasancewa a yau Laraba.
Shima mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Ado Riruwai, ya tabbatar da cewar kungiyarsu ta rufe dukkanin wasu ofisoshin gwamnati dake jihar Kano, domin tabbatar da yajin aikin gargadin.