Connect with us

News

Yan Majalissar Dokoki  Suna Maida Martani Ga Masu Sukar Shirin Sayen Motocin Alfarma

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Duk da kurar da ta taso a cikin ‘yan kwanakin nan, majalisar dattawan na bayar da hujja da kare matakinta na shirin sayen motocin alfarma akan Naira miliyan 160 kowacce Mota.

Advertisement

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a Abuja, Shugaban Kwamitin Ayyuka na Majalisar Dattawa, Sunday Karimi, ya ce shugabannin majalisun biyu sun yanke shawarar sayen motocin alfarma ga ‘yan majalisar ne saboda dorewa da kula da su na tsawon shekaru hudu.

Shugaban kungiyar Pan Niger Delta, PANDEF Yana  Neman A Cire Wasu Jahohi Uku Daga Hukumar NDDC.

Karimi ya ci gaba da cewa ‘yan Najeriya na sa ido akan ‘yan majalisa amma sun manta da ministoci domin a cewarsa wasu ministocin suna da motocin alfarma sama da uku kuma ba a tuhumarsu.

Advertisement

 

Wannan dai na zuwa ne kwanaki bayan da jama’a suka yi ta cece-kuce kan yadda ‘yan majalisar za su sayi motoci wanda farashinsu ya kai naira miliyan 160 kowacce.

Advertisement

A Wani labarin kuma Shugaban kungiyar Pan Niger Delta, PANDEF Yana  Neman A Cire Wasu Jahohi Uku Daga Hukumar NDDC.

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending