News
Shugaban kungiyar Pan Niger Delta, PANDEF Yana Neman A Cire Wasu Jahohi Uku Daga Hukumar NDDC.
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban kungiyar Pan Niger Delta, PANDEF, Cif Edwin Clark, ya yi kira da a cire jihohin Abia, Imo, da Ondo daga hukumar raya yankin Neja Delta, ta NDDC.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi gyaran fuska ga doka ta 2000 da ta kafa hukumar.
Kungiyoyin Kwadago Ma Kasa Na Sake Sabon Shirin Tafiya Yajin Aiki
Clark ya ce gyaran dokar zai bada dammar cire Jihohin da ba na Neja Delta mai arzikin man fetur ba, kamar Abia, Imo da Ondo daga jihohi tara da suke karkashin NDDC wadanda su ne, Ondo, Edo, Delta, Bayelsa, Ribas, Imo, Abia, Cross River da Akwa Ibom.
Dattijon wanda ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Talata, ya bayyana cewa shigar jihohin uku a cikin hukumar wata matsala ce ta siyasa.
A Wani labarin kuma Kungiyoyin Kwadago Ma Kasa Na Sake Sabon Shirin Tafiya Yajin Aiki
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
