News
Kungiyoyin Kwadago Ma Kasa Na Sake Sabon Shirin Tafiya Yajin Aiki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyoyin kwadago ta bayyana rashin gamsuwarta da tafiyar hawainiya wajen aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna da ta rattaba hannu da gwamnatin tarayya don dakile yajin aikin da ta shirya tsunduma a fadin kasarnan.
A sassan jihohin Najeriya kungiyoyin NLC da TUC sun ce rashin aiwatar da yarjejeniyar kafin wa’adin ranar 30 ga watan Oktoba na iya kaiwa ga babu wani zabi illa dakatar da ayyuka da sauran al’amuran yau da kullum a fadin Najeriya wanda tun sun fara hada kan mambobinsu a fadin kasarnan.
Rundunar Soji Sun Kashe ‘Yan Fashin Daji Da Dama, Sun Kwato Makamai A Sokoto
Da aka tambaye shi ranar Talata ko ‘yan kwadago sun gamsu da aiwatar da yarjejeniyar, shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NLC, Benson Upah, ya ce, “A’a. Gwamnati na iya yin yunkuri mafi kyau da sauri.
Shima da yake zantawa da manema labarai, shugaban kungiyar TUC na jihar Ogun, Akeem Lasisi ya bayyana cewa, aiwatar da mafi yawan yarjejeniyoyin suna kan teburin gwamnatin tarayya, inda ya kara da cewa babban abin da ya fi muhimmanci ga jahohi da kananan hukumomi shi ne biyan albashin ma’aikata.
A wani labarin kuma Rundunar Soji Sun Kashe ‘Yan Fashin Daji Da Dama, Sun Kwato Makamai A Sokoto
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
