News
Rundunar Soji Sun Kashe ‘Yan Fashin Daji Da Dama, Sun Kwato Makamai A Sokoto
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dakarun sojoji da ke karkashin Bataliyar 8 a ranar Talata sun samu nasarar hallaka ‘yan fashin daji da dama tare da kwato makamai daga hannunsu a jihar Sokoto.
Majalissar Dokokin Ondo Ta Cigaba Da Shirin Tsige Mataimakin Gwamna
A wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na sojoji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce, sojojin sun kaddamar da samamen ne a kauyen Tukandu, inda suka afka wa ‘yan fashin daji da suka yi kaurin suna wajen addabar jama’a da ayyukansu na ta’addanci a yankin baki daya.
Kutsen Da Wasu Jiragen Ruwan Philippines Suka Yi A Ren’ai Jiao Dake Tekun Kudancin Kasar Sin Ya Bayyana Makircin Amurka
An Gudanar Da Taron Manyan Jami’ai Karo Na 16 Na Dandalin FOCAC
A bisa wannan kokarin, ya ce, sojojin sun hallaka ‘yan ta’addan yayin da wasu suka tsira da raunukan harbin bindiga a jikinsu.
Bayan samamen da suka yi, sojoji sun kwato bindiga kirar AK-47 guda uku, bindiga kirar PKT, alburusai masu guda 125, bama-bamai guda biyu, da kuma mashina guda tara.
Shugaban sojojin Nijeriya, Taoreed Lagbaja, ya jinjina wa kokarin sojojin, inda ya nemi su kara himma da kwazo har zuwa lokacin da za a tabbata da kakkabe dukkanin ‘yan ta’addan da suke addabar jama’a a kasar nan.
A wani labarin kuma Majalissar Dokokin Ondo Ta Cigaba Da Shirin Tsige Mataimakin Gwamna
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
