Connect with us

News

Rundunar Soji Ta Yi Magana A Kan Ma Su Fita Zanga-Zanga Da Tutar Kasar Rasha

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Babban hafsan rundunar tsaro ta kasa (CDS), Janar Christopher Musa, ya bayyana ma su fitowa zanga-zanga dauke da tutar kasar Rasha a matsayin maciya amanar kasa.

Advertisement

Da yake magana da manema da labarai a Aso Rock jim kadan bayan kammala wani taro na gaggawa a kan tsaro tare da shugaba Tinubu, Janar Musa ya bayyana cewa doka za ta yi aiki a kan wadanda suka aikata hakan.

An Kama Telan Dake Dinka Tutar Rasha Ga Masu Zanga-zanga A Kano

Da ya ke mayar da martani a kan ma su kiran sojoji su yi juyin mulki, Shugaban Sojojin ya bayyana cewa sojojin Nigeria sun rungumi mulkin dimokradiyya a saboda haka juyin mulki ba zai yiwu ba.

Advertisement

“A kan maganar juyin mulkin, ina son fadin cewa Nigeria kasa ce mai cin gashin kan ta wacce kuma take kan tsarin dimokradiyya wanda mu a matsayinmu na jami’an tsaro ya kamata mu tabbatar ya dore.

“Ba zamu yarda da duk wani kira ko yunkuri na kawo canjin gwamnati ba ta hanyar dimokradiyya ba. Mun rungumi dimokradiyya kuma zamu cigaba da kare ta.”

Advertisement

“Su kuma ma su daga tutar wata kasar, idan ka duba za ka ga cewar yara ne da ake ingiza wa. Muna bin diddigin wadanda suke daukar nauyin su. Mun gano wuraren da ake aikata hakan kuma za mu dauki mataki mai tsauri a kan hakan,” a cewar Janar Musa.

Janar Musa ya kara da cewa shugaban kasa, Bola Tinubu, ya basu umarnin cewa kar su bari wasu mutane su kawo tarnaki ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin Nigeria.

Advertisement

Kazalika, ya bayyana cewa sun bawa shugaba Tinubu tabbacin cewa rundunar soji za ta hada kai da sauran hukumomin tsaro na kasar nan domin tabbatar da zaman lafiya a fadin kasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending