News
Cikin Shekara Biyar An Sace Danyen Mai Na Trilliyan 4. – NEITI
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar da ke binciken yadda aka kashe kudaden da aka samu daga ma’adanan man fetur a Najeriya, NEITI,, ta ce an sace danyen mai na sama da Naira trilliyan 4.3 a hare-haren fasa bututun mai guda dubu 7 da 143 a cikin shekaru biyar.
Babban sakataren zartaswa na hukumar, Ogbonnaya Orji ne ya bayyana hakan a taron fasahar bututun mai na kasa da kasa da aka yi a Abuja ranar Litinin.
Orji ya ce satar mai wani al’amari ne na gaggawa da ke haifar da babbar barazana ga hako man fetur da kuma yin amfani da shi tare da babbar illa ga ci gaban tattalin arziki da kasuwanci na kamfanonin mai.
Ya yi zargin cewa da yawa daga cikin ‘yan kungiyar dake harkokin bututun mai suna da hannu kai tsaye da kuma a fakaice wajen samar da kwarewa da ilimin da ake bukata wajen satar mai.
A wani labarin kuma Hukumar Hisbah Na Tayin Aurar Da ‘Yan TikTok A Jahr Kano
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
