News
Fitaccen dan wasan kwaikwayon Hausa Samanja ya rasu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Fitaccen dan wasan kwaikwayo na Hausa Alhaji Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja ya rasu yana da shekara 81.
Bayanai daga iyalansa sun ce ya rasu ne da sanyin safiyar Lahadi a birnin Kaduna da ke arewacin Nijeriya.
Gwamnatin Jahar Osun Ta Karyata Batun Karin Albashin 25,000 Ga Ma’aikata
Alhaji Usman Baba Pategi ya taka rawa a matsayin Samanja Mazan Fama a wasan kwaikwaiyon da aka kwashe shekara da shekaru ana gabatarwa a Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna.
An haife shi ranar 20 ga watan Mayu na shekara 1942 a Masarautar Pategi da ke Jihar Kwara.
Ɗa ne ga marigayi Etsu Usman Patako na Pategi.
Usman Baba Pategi ya yi karatun Firamare da Sakandare a Pategi da Ilorin.
A shekarun 1960 ya shiga Rundunar Sojin Nijeriya inda ya rike mukamin Kyaftin a lokacin yakin basasar kasar.
Ya yi ritaya a shekarar 1985 inda ya soma wasan kwaikwayo a Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna, lamarin da ya ba shi damar rubutawa da kuma bayar da umarni na wasannin kwaikwayo. An fi saninsa a matsayin Samanja Maza Fama.
Baba Pategi yana da mata biyu da ‘ya’ya.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News4 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
