News
Gwamnatin Jahar Osun Ta Karyata Batun Karin Albashin 25,000 Ga Ma’aikata
DAGA KABIRUBASIRU FULATAN
Gwamnatin jihar Osun ta musanta rahotannin da ke cewa ta kara alawus-alawus ga ma’aikatan jihar da naira 25,000.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a, Kolapo Alimo ya sanya wa hannu a ranar Lahadi gwamnatin jihar ta bayyana wannan labarin a matsayin labaran karya da kuma wani sharri da aka kirkira domin yaudarar al’ummar jihar.
Saudi Arabia zata zuba jari a matatun man Najeriya guda 4 domin farfado da su
Har ila yau, ta bayyana bayanan a matsayin na hannun miyagu da suka dukufa wajen samar da wata baraka tsakanin gwamnati da ma’aikatan jihar.
An jawo hankalin gwamnatin jihar Osun kan batun alawus-alawus na N25,000 ga ma’aikata a watan Nuwamba a halin yanzu.
A kan wannan al’amari, gwamnatin jihar Osun ta yi watsi da shi inda tace an kirkireshi don yaudarar ma’aikata da mutanen jihar da ba su ji ba ba su gani ba.
Don haka gwamnatin Sanata Ademola Adeleke tana amfani da wannan kafar don tabbatar wa jama’a, musamman ma’aikatan gwamnati cewa,batun da ake magana a kai abu ne da wasu suka yi niyyar samar da wata baraka a tsakanin gwamnatin Sanata Ademola Adeleke da ma’aikata.
Muna gaggauta jaddada cewa idan har za a samu karin alawus, ya kamata ma’aikatan gwamnati a jihar Osun su tabbatar da cewa gwamnatin Sanata Ademola Adeleke za ta bayyana hakan ta kafafen yada labarai.
DAILY POST ta tattaro cewa a karshen makon da ya gabata wani rahoto ya fito yana bayyana cewa gwamnatin jihar ta kara karin N25,000 ga albashin ma’aikatan jihar Osun.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
