News
Saudi Arabia zata zuba jari a matatun man Najeriya guda 4 domin farfado da su
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kasar Saudi Arabia ta ce zata zuba jari a matatun man Najeriya guda 4 da ake kokarin farfado da su domin tace mai a cikin gida, tare da samarwa kasar isassun kudaden kasashen ketare na dala domin magance karancin su da yanzu haka ya jefa harkokin kasuwanci cikin halin kakanikayi.
Yarima Muhammad bin Salman ya bayyana haka sakamakon tattaunawar da suka yi da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a wajen taron zuba jari na Saudiya da kasashen Afirka dake gudana a birnin Riyadh.
Mutane 140 ne suke jira a zartar musu da hukuncin kisa a Kano
A karkashin jagorancin shugaba Tinubu, Najeriya ta kaddamar da sauye sauye masu tsauri, cikin su harda cire tallafin man fetur da kuma hade musayar kudaden ketare domin taimakawa masu harkokin kasuwanci, amma kuma har ya zuwa wannan lokaci ba’a kaiga cimma biyan bukata ba na kawar da yadda ake sayar da kudaden kasashen ketaren a farashi daban
Ministan yada labaran Najeriya, Mohammed Idris yace gwamnatin Saudi Arabia tayi alkawarin samar da kudaden da ake bukata domin magance matsalar karancin kudaden ketaren da ake matukar bukatar su domin hada hadar kasuwanci.
Idris ya kuma tabbatar da kulla yarjejeniyar da kasashen biyu suka yi, wanda zai baiwa kamfanin man Saudiya na Aramco damar zuba jari a matatun man Najeriya guda 4 wadanda ake saran kammala gyaransu nan da shekaru 3 masu zuwa.
Najeriya wadda itace kasar da tafi kowacce arzikin mai a nahiyar Afirka, na kokarin ganin ta koma tace man ta a cikin gida, amma kuma kokarin farfado da matatun na ci gaba da fuskantar matsaloli.
A wani labarin kuma Mutane 140 ne suke jira a zartar musu da hukuncin kisa a Kano
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News4 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
