Connect with us

News

Mutane 140 ne suke jira a zartar musu da hukuncin kisa a Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Jihar Kano a arewacin Nijeriya ta ce mutum dari da arba’in ne suke jira a zartar musu da hukuncin kisa bayan kotuna sun same su da laifuka.

Kakakin hukumar, Musbahu Kofar-Nassarawa ne ya bayyana haka ranar Asabar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya rawaito.

Ya kara da cewa mutanen sun hada da maza da mata.

Ɗan wasan baya na Portugal Pepe ya kafa sabon tarihi a gasar Zakarun Turai

“Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Kano ba ta da mai rataye mutane saboda wuri ne na daure mutanen da suka aikata matsakaitan laifuka,” in ji Kofar-Nassarawa.

Advertisement

 

Ya kara da cewa gwamnonin da suka mulki jihar sun gaza sanya hannu kan takardun zartar da hukuncin kisa ko kuma su mayar da hukuncin na daurin rai-da-rai.

“Wasu gwamnonin suna amfani da damar da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba su domin sakin mutanen da ke kurkuku bisa samun shawarwari daga Majalisar Bayar Da Shawara kan yi wa fursunoni afuwa domin rage cunkoso a gidajen yari,” a cewar Musbahu Kofar-Nassarawa.

 

Trt Word 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending