Connect with us

News

Kungiyar Hamas ta lalata motoci 160 na sojojin Isra’ila

Published

on

DAGA UASIR SANI ABDULLAHI

Sashen soji na kungiyar Hamas ya ce ya lalata motoci 160 na dakarun Isra’ila tun lokacin da suka kaddamar da hare-hare ta kasa a Gaza, yana mai cewa ya lalata motoci 25 a cikin kwana biyu da suka gabata.

Hakan na faruwa ne a yayin da rundunar sojin Isra’ila ta ce an kashe dakarunta 43 tun da ta kaddamar da kutse ta kasa a Gaza.

An Sace Jami’in Hukumar INEC A Bayelsa

A wani labarin kuma Dakarun Isra’ila sun kaddamar da jerin hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na Gaza, a cewar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da Tsaron Kasa ta Gaza.

Ma’aikatar ta fitar da sanarwa da ke bayani dalla-dalla kan jerin hare-hare ta sama da dakarun Isra’ila suka kai a sassa daban-daban na Gaza.

“Jiragen sama na dakarun mamaya sun kaddamar da jerin hare-hare a harabar Mahadar Saraya da ke Birnin Gaza,” in ji ma’aikatar, tana mai karawa da cewa Isra’ila ta kuma “kaddamar da samame a yankin Tal al Zaatar da kuma Asibitin Indonesian Hospital da ke arewacin Gaza.”

Advertisement

Ta kara da cewa jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a arewaci da tsakiyar Birnin Gaza da yankin Al Nasr da kuma yankunan kusa da garin Jabalia da ke arewacin Gaza.

 

Trt Word

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending