News
An Sanya Ladan Naira Miliyan 5 Ga Wanda Ya Bankado Fursunonin Da Suka Tsere
Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya ta bayyana bayar da ladan Naira miliyan biyar ga duk wanda ya bayar da sahihin bayani da zai kai ga kamo fursunonin da suka tsere daga gidan gyaran hali na Ilesha da ke Jihar Osun.
Wata sanarwa da Mataimakin Kwamanda kuma Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Umar Abubakar ya fitar a ranar Laraba ta ce fursunoni bakwai ne suka tsere daga gidan gyaran halin, kuma ana ci gaba da bincike don gano inda suka shiga.
Hukumar ta bukaci jama’a da su taimaka wajen samar da duk wani bayani da zai taimaka wa jami’an tsaro kama fursunonin, tana mai tabbatar da cewa za a kiyaye sirrin wadanda suka bayar da bayanan.
An fadi cewa jama’a za su iya tuntubar hukumar ta hanyar imel kamar haka:
complaintresponsedesk@corrections.gov.ng
info@corrections.gov.ng
Hukumar ta ce hadin kan jama’a na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin kasa.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
