News
An Gano Hamdiyya A Zamfara Cikin Mawuyacin Hali
Fitaccen lauya Barista Abba Hikima ya bayyana cewa an gano Hamdiyya Sidi, matashiyar da ta ɓace a ranar Talata, a Babban Asibitin Bakura da ke Jihar Zamfara.
Hamdiyya ’yar asalin Jihar Sakkwato ce, wacce ke fuskantar shari’a da gwamnatin jiharta kan zargin yin kalaman da ake ganin na tunzura jama’a ne.
Gwamnatin Kano ta Shiryawa Ma’aikatan Yada Labarai Na Kananan Hukumomi Bitar Kwana 2
A cewar Barista Hikima, Hamdiyya ta ɓace ne da safiyar Talata bayan ta fita cefane da misalin ƙarfe 10 na safe, lamarin da ya tayar da hankula a kafafen sada zumunta, inda jama’a da dama suka nuna damuwarsu.
Bayanai sun nuna cewa ɓacewar Hamdiyya ta ja hankalin ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta duniya, Amnesty International, wadda ta bukaci jami’an tsaro su gaggauta neman inda take.
Sai dai a yammacin ranar Laraba, Barista Hikima ya ce an gano ta cikin mawuyacin hali amma tare da jami’an tsaro.
“Mun samu labarin cewa Hamdiyya na Babban Asibitin Bakura a Zamfara. Tana cikin mawuyacin hali, amma tana tare da jami’an tsaro. Ya tabbata an sace ta. Alhamdulillah ala kulli halin,” in ji shi.
Lamarin ya ƙara jaddada muhimmancin tsaro da kariya ga masu fuskantar matsin lamba ko barazana a sakamakon ra’ayoyinsu.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
