Connect with us

News

Gwamnatin Kano ta Shiryawa Ma’aikatan Yada Labarai Na Kananan Hukumomi  Bitar Kwana 2

Published

on

1747841155969

Gwamnatin Jihar Kano ta shirya bitar kwanaki biyu domin inganta kwarewar ma’aikatan yada labarai daga kananan hukumomi 44 da kuma shugabannin sashen labarai na gidajen rediyo a fadin jihar.

An gudanar da taron horaswar ne a dakin taro na Grand Central Hotel da ke Bompai, Kano, karkashin hadin gwiwar Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida da Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu.

Kotu Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Tiamin Hospital Diyyar Naira Biliyan 2.6

Taken taron ya kasance: “Inganta Kwarewar Sadarwa da Hadin Kai da Masu Ruwa da Tsaki Domin Isar da Bayani Ingantacce a Matakin Kasa.”

Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce horaswar na da matukar muhimmanci domin bunkasa isar da sahihan bayanai daga gwamnati zuwa ga al’umma.

“Ma’aikatan labarai a matakin kasa suna taka muhimmiyar rawa wajen hada gwamnati da jama’a. Don haka wajibi ne su rika aikinsu da gaskiya da inganci,” in ji Waiya.

Ya kuma bukaci jami’an da su rika hada kai da ’yan jarida da masu yada labarai a kafafen sada zumunta domin tabbatar da gaskiya da daidaito a dukkan bayanan gwamnati.

Advertisement

A nasa bangaren, Babban Sakataren Ma’aikatar Yada Labarai, Malam Adamu Muhammad, ya ce an shirya taron ne domin kara wa jami’an ilimi da kwarewa kan hanyoyin isar da sakonni da suka shafi gwamnati.

“Jami’an bayar da bayani su ne murya ta farko da gwamnati ke amfani da ita wajen isar da shirye-shiryenta,” in ji shi.

Haka kuma, Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Hon. Tajudeen Othman, ya ce matakin kasa na taka rawa wajen tabbatar da shugabanci nagari. Ya bukaci jami’an labarai da su rika yada sahihan bayanai cikin lokaci da la’akari da al’adun jama’a.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending