Connect with us

News

Hukumar Kula da Yanayi ta kasa NiMet ta yi hasashen hasken samun rana da hazo a fadin Najeriya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen cewa za fuskanci hasken rana da kuma hazo daga ranar Juma’a zuwa Litinin a faɗin ƙasar.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce cikin jihohin da za su fuskanci hazon sun haɗa da Yobe, Borno, Jigawa, kuma Kano

Advertisement

A Janye ‘Yan sandan Da Ke Aikin Kare Masu Hannu Da Shuni.

“Za a kuma fuskanci gajimare tare da hasken rana a jihohin kudu tare da yanayin hadari a kan yankunan bakin teku,” in ji NiMet.

Ta ce ana sa ran fuskantar hasken rana tare da gajimare a faɗin jihohi da yiwuwar samun tsawa a sassan Edo, Bayelsa, Akwa-Ibom, Delta, Cross River da kuma Rivers nan gaba a yau.

Advertisement

Har ila yau, NiMet ta ce za a samu hazo mai cike da ƙura a jihohin arewa a ranar Asabar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending