Connect with us

News

Yan jaridar BBC sun zargi kafar watsa labaran da goyon bayan Isra’ila a yakin da take yi da Falasdinawa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

‘Yan jaridar BBC sun soki kafar watsa labaran da ke Birtaniya bisa “nuna goyon baya ga Isra’ila da kuma rashin bayar da isassun rahotanni kan fararen-hula Falasdinawa idan aka kwatanta da Isra’ilawa a shirye-shiryenta game da rikicin Isra’ila da Falasdinawa,” kamar yadda Al Jazeera ta rawaito.

“BBC ta gaza yin binciken kwakkwafi game da ikirarin da Isra’ila ke yi, ba ta bayar da sahihin labari, don haka ba ta taimaka wa masu bibiyarta fahimtar keta haddin da ake yi a Gaza,” a cear wata wasika da ma’aikatan BBC takwas suka aika wa Al Jazeera ranar Alhamis.

Advertisement

Dakarun tsaron Najeriya sun kashe Ƴan ta’adda 99 sun kama wasu 198 – Hedikwatar tsaro

A wasikar, ‘yan jaridar na BBC sun zargi kafar watsa labaran da suke yi wa aiki da goyon bayan Isra’ila.

Sun yi zargin cewa a yayin da BBC ta nuna babu sani babu sabo a bayar da rahotanni kan zargin da ake yi wa Rasha na aikata laifukan yaki a Ukraine, a game da yakin Isra’ila da Falasdinawa tana “baki-biyu” musamman kan yadda take rawaito ukubar da fararen-hula a Gaza suke ciki.

Advertisement

Kazalika tana tantama kan yawan Falasdinawa da aka kashe tun da Isra’ila ta kaddamar da yaki a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba.

Wasikar ta ambato ‘yan jaridar BBC suna cewa kafar watsa labaran tana amfani da kalmomi irin su “kisan kare-dangi” da “cin zarafi” ne kawai idan ya shafi Hamas, inda take bayyana kungiyar ta Falasdinawa a matsayin daya tilo da ta haifar da rikici a yankin.

Advertisement

 

 

Advertisement

TRT WORD

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending