Connect with us

News

Bashin N87trn: SERAP ta nemi Bankin Duniya da ya dakatar da lamuni ga jihohi 36 na Najeriya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Kungiyar SERAP ta kai kukan wasu jihohin Najeriya ga Bankin Duniya, dangane da yadda suke kashe maƙudan kuɗaɗen da bankin ke ba su da sunan lamuni, ta hanyar ragabza da ɓarusa.

SERAP ta yi kukan cewa yayin da jihohi da yawa ba su iya biyan albashi da alawus-alawus na ma’aikatan su, su kuma gwamnonin jihohin su raja’a wajen taɓargaza da kuɗaɗen da suka kamata a yi wa al’ummar jihohin ayyukan raya jihohi da su.

Advertisement

Duk Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta, Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 

“Miliyoyin ‘yan Najeriya na fama da ƙarancin ababen more rayuwa, rashin ilmi mai inganci da rashin kulawa a fannin harkokin lafiya.

 

Advertisement

“Gwamnoni da yawa na kashe kuɗaɗe, ciki har da kuɗaɗen da Bankin Duniya ke ba su lamuni, wajen sayen motoci masu tsada, motoci masu sulke, kayan alfarma, bukukuwa da taruka marasa amfani.”

 

Advertisement

Cikin ƙorafe-ƙorafen da SERAP ta yi, ta bayyana wa Bankin Duniya yadda yawancin jihohi ke kashe kasafin jihohin wajen sayen kayayyakin da ba su da tasiri ga rayuwar talakawan jihar.

 

Advertisement

SERAP ta yi wa Bankin Duniya dalla-dallar yadda jihohin Najeriya ke kashe kuɗaɗen su. Ciki har da yadda Jihar Bayelsa ta kashe Naira biliyan 58.26 kan walwala, bukukuwan rufe gawa, tarukan godiya ga Ubangiji da shagalin bikin aure.”

 

Advertisement

“Jihar Legas an ware Naira miliyan 440 don sayen mota mai sulke ga Shugaban Ma’aikatan Jihar Legas.

 

Advertisement

Kan haka ne SERAP SERAP ta roƙi Bankin Duniya ya daina bayar da ramce ga jihohin Najeriya 36.

 

Advertisement

Kungiyar Sa-ido da Bin Diddigin Dimokraɗiyya, SERAP, ta roƙi Bankin Duniya ya dakatar da bayar da ramce, lamuni ko basussuka ga ɗaukacin jihohi 36 na Najeriya.

 

Advertisement

Har ila yau, SERAP ta kuma roƙi Shugaban Bankin Duniya, cewa kada ya sake bayar da kuɗaɗen ga jihohin, har sai gwamnonin Najeriya 36 sun gamsar da Bankin Duniya irin abubuwan inganta rayuwar al’ummar da suka yi da kuɗaɗen.

 

Advertisement

Haka kuma dai SRRAP ta ƙara yin kira cewa Shugaban Bankin Duniya Ajay Banga ya kafa binciken tabbatar da yadda jihohin na Najeriya ke kashe kuɗaɗen da Bankin Duniya ko wasu cibiyoyin hada-hadar da ke ƙarƙashin Bankin Duniya ke bai wa jihohin.

 

Advertisement

SERAP ta ce, “domin akwai ƙorafe-ƙorafen cewa jihohi da dama su ke daƙashama, bushasha, ragabza, taɓargaza da ɓarusa da kuɗaɗen da suke karɓowa.

 

Advertisement

SERAP ta ce duk wata takarar neman lamunin Bankin Duniya da wasu gwamnoni su ka aika a yanzu a Bankin Duniya, to a jingine batun, har sai gwamnonin sun yi bayanin yadda suka kashe kuɗaɗen da aka karɓa a baya, waɗanda ake neman karɓa kuma a yanzu a dakatar da batun bayarwar.”

 

Advertisement

Cikin kuɗaɗen da ake zargin wasu jihohin na ɓarusa da su, har da wasu a su ke karɓa daga irin basussukan da Gwamnatin Tarayya ke karɓa daga Bankin Duniya, ta na raba wa jihohi.

 

Advertisement

Cikin wata wasiƙa da SERAP ta aika wa Mataimakin Darakta Kolawole Oluwadare, a ranar Asabar, 25 ga Nuwamba, ƙungiyar ta ce, “Kada Bankin Duniya da abokan hada-hadar bankin su riƙa ɗibar kuɗaɗe ta na bai wa jihohi, alhali kuma ƙiri-ƙiri ana gani ba su komai da kuɗaɗen, sai bushasha da ɓarusa su ke yi da kuɗaɗen.”

 

Advertisement

“Ofishin Kula da Basussuka na Najeriya, DMO ya ce ana bin ɗaukacin jihohin Najeriya 36 ya kai Naira 9.17. Ita kuma Gwamnatin Tarayya ana bin ta bashin Naira tiriliyan 78.2.”

 

Advertisement

“Muna kira ga Bankin Duniya ya aiko da masu bincike na musamman domin su bi diddigin yadda jihohin Najeriya 36 ke kashe kuɗaɗen da ake ba su domin su yi wa mutanen karkara ayyukan raya ƙasa.

 

Advertisement

“Saboda asusun bankunan jihohin Najeriya 36 cikin sirri ake tafiyar da su, ba su gudanar da komai ƙeƙe-da-ƙeƙe. Da yawa daga cikin su ba su bai wa ‘yan jarida damar sanin yadda ake kashe kuɗaɗen haƙƙin jama’a a jihohin.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending