News
Gobara ta Tashi a Ofishin Bankin Duniya dake Jihar Yobe
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gobara ta kone ofishin kula da shirin farfado da rikici da ake kira Multi-Sectoral Crisis Recovery (MCRP) wanda bankin duniya ke taimakawa shirin.
Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, gobarar ta tashi ne a ofishin da ke kan titin Potiskum da misalin karfe 12:40 na ranar Lahadi.
Bashin N87trn: SERAP ta nemi Bankin Duniya da ya dakatar da lamuni ga jihohi 36 na Najeriya
Har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga ofishin hadin gwiwa kan abin da ya haddasa barkewar tashin gobarar.
Tuni dai jami’an kashe gobara na jihar Yobe Suka jajirce wajen kashe wutar da ta tashi.
A wani labarin kuma Bashin N87trn: SERAP ta nemi Bankin Duniya da ya dakatar da lamuni ga jihohi 36 na Najeriya
Wata ƙungiyar bayar da agaji ta addinin kirista ta ce mayaƙa masu alaƙa da kungiyar Al-Qaeda sun sako wani BaJamushe ɗan mishan da suka kama shekara ɗaya da ya wuce a kasar Mali.
Kungiyar mai suna Missionaries for Africa ta ce an yi awo gaba da Fr. Hans Joachim Lohre ne a babban birnin kasar Bamako.
Babu wasu bayanai game da yadda aka yi aka sako shi kuma gwamnatocin ƙasashen Jamus da Mali ba su komai ba kan batun.
Fr. Lohre ya kwashe shekaru 30 a Mali yana koyar da darussan hulda tsakanin addinai a wata makaranta mai koyar da darussan addinin musulunci da kiristanci a haɗe.
Satar mutane ne ba bakon lamari ba ne a Mali amma ba kasafai akan yi hakan a babban birnin kasar ba.
