Connect with us

News

NDLEA ta Cafke Tan Biyu Na Haramtattun Muggan Kwayoyin a Wasu Jihohi Bakwai

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta kama sama da tan biyu na haramtattun Muggan Kwayoyin a fadin jihohin Legas, Ogun, Edo, Ekiti, Anambra, Ondo da Kogi a cikin makon da ya gabata.

Advertisement

Kakakin hukumar, Mista Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja cewa jami’an hukumar sun kai farmaki a wani kantin sayar da kayayyaki da ke Obi Camp a karamar hukumar Owan ta Yamma a Edo a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba.

Gobara ta Tashi a Ofishin Bankin Duniya dake Jihar Yobe 

Sun kama kilogiram 338kg na tabar wiwi da aka boye a cikin buhunan gawayi a samamen.

Advertisement

 

Jami’an NDLEA sun kuma kai samame dajin Ikhin da ke karamar hukumar Owan ta Gabas a jihar Edo a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, inda suka kama kilogiram 235 na sinadari Mai sa maye.

Advertisement

 

“An kama wanda ake zargi, Onah Ikechukwu (32) a Jattu da ke karamar hukumar Etsako ta Yamma a jihar a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba.

Advertisement

 

“Jami’an sun kwace fakitin tramadol guda 11,690, kwalaben codeine 295 da kuma Molly, tabar wiwi da kuma Methamphetamine iri-iri daga hannun wanda ake zargin.

Advertisement

 

“Wani harin da aka kai a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba a titin Enu-Owa, dake Legas Island, ya kai ga kama ampoules na allurar pentazocine guda 40,500 da kwayoyin tramadol 440,000 a wani kantin sayar da magunguna da ke alaka da wani Ebuka Amechi.

Advertisement

 

A ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwamba, jami’an NDLEA a Ogun sun kama wasu mutane biyu – Adamu Ibrahim da Nura Sani a garejin tirela na Ileke, kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Advertisement

 

Shugaban Hukumar NDLEA, Brig. Janar Buba Marwa, ya yabawa jami’an hukumar kan mutanen da suka kama.

Advertisement

 

Ya umarce su da su kasance a faɗake kuma su ninka ƙoƙarinsu, musamman ganin yadda ƙungiyoyin masu aikata laifuka suka yunƙura don samun kuɗi cikin gaggawa a shirye-shiryen lokacin Yuletide. NAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending