News
Tinubu zai gabatar wa majalisa kasafin kuɗi na 2024 Ranar Laraba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar Zartarwa ta amince da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2024.
Dangane da hakan ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar wa Majalisar Tarayya kasafin a ranar Laraba mai zuwa.
Sakataren bincike da yada labarai a Majalisar Tarayya, Dokta Ali Barde Umoru ya tabbatar da haka a yammacin yau.
A kunshin kasafin da Majalisar Zartarwar ta amince da shi, an tsaida farashin gangar mai a kan $73.96 da lissafin cewa za a rika hako ganguna miliyan 1.78 a rana da kuma farashin duk dala guda a kan N750.
Wannan ne cikakken kasafi na farko da Bola Tinubu zai gabatar wa majalisar tun bayan rantsar da shi a watan Mayun da ya wuce.
Gabatar da kasafin ya nuna cewa Mista Tinubu zai ci gaba da tafiyar da tsarin kasafin kudin daga Janairu zuwa Disamba kamar yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar.
A wani labarin kuma Tinubu ya nada sabon kwamitin gudanarwa na NNPCL
Ministan yaɗa labaran Saliyo ya bayyana cewa, hare-haren da wasu masu dauke da makamai suka kai a jiya Lahadi kan wasu muhimman cibiyoyin gwamnati, sun kasance tsararrun hare-hare a kan harkokin tsaron kasar.
Sai dai Chernor Bah ya shaida wa BBC cewa masu laifin da suka hadar da tsoffin sojoji da kuma wasu masu kaki a yanzu sun gaza cimma burinsu.
Ya ce ana yi wa waɗanda aka kama tambayoyi.
Ana ci gaba da farautar sauran ‘yan ta-da-kayar-bayan da kuma wasu fursunoni da suka tsere a lokacin da aka kai hari a gidajen yari.
An ɗage dokar hana fita a fadin kasar, amma har yanzu dokar na ci gaba da aiki da daddare.
