Connect with us

News

Fiye da mutum 20 sun mutu sakamakon fashewar bututun ɗanyen mai a jihar Ribas

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRAD’YAN

 

Wata fashewa da ta faru bayan fasa wani bututun ɗanyen mai da ke ƙarƙashin ƙasa a ƙaramar hukumar Ogba/Egebema/Ndoni da ke jihar Ribas ta halaka aƙalla mutum 20.

Bbc ta ruwaito cewa Lamarin ya faru ne a ƙarshen makon daya gabata a ƙaramar hukumar da ke zama ɗaya daga cikin cibiyoyi masu arzikin mai da iskar gas a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Kuɗaɗenku ba sa fuskantar haɗari a banki – CBN

Rahotanni na cewa an kwantar da mutanen da suka samu ƙuna a asibitoci da dama a garin.

 

Advertisement

Zuwa yanzu, babu tabbacin abin da ya jawo fashewar da ta haddasa gobara da kuma adadin mutanen da suka mutu.

Shugaban matasan yankin ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da matasan suke raba ɗanyen man da aka sato a jarkoki.

Wani ɗan jarida ya tabbatar cewa gobarar ta tashi lokacin da matasan suke rige-rigen kwasar ɗanyen man daga wani bututu da ke ƙarƙashin ƙasa a lokacin da gobarar ta tashi.

A wani labarin kuma Kuɗaɗenku ba sa fuskantar haɗari a banki – CBN

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

Advertisement

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending