News
Shekarau Ya Buƙaci Abba Da Gawuna Su Amince Da Hukuncin Da Kotun Ƙoli Za Ta Sanar
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya yi kira da mabiya da shugabannin NNPP da na APC su rungumi hukuncin da kotun kolin ƙasar za ta yanke a matsayin ƙaddara.
Shekarau ya yi wannan kira ne a wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels a wani shirin siyasa.
Shekarau ya ce, ya yi imani da cewa babu wani zagi ko cin zarafi ko kuma kalaman ɓatanci da za su sauya hukuncin da ko tu za ta yanke, ko kuma su sa a bai wa wani nasara a yayin hukuncin.
Tun a watan Maris ɗin 2023 ne ake ta sa-toka-sa-katsi a kotu tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma Nasiru Yusuf Gawuna kan kujerar gwamnan jihar Kano.
Shekarau ya ce “duk mutumin da ke bin siyasa ta, yasan siyasar zaman lafiya da kwanciyar hankali nake yi. Ina ɗaukar abokan siyasata abokaina ba tare da duba banbancin siyasa ba.
A wani labarin kuma Masarautar Saudiyya Ta Kere Elon Musk Da Bill Gates Arziki
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day agoJam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
