Connect with us

News

Wani Matashi A Gombe Ya Kirkiri Injin Ban Ruwa Mara Amfani Da Fetur Ko Hasken Rana

Published

on

Inji amfani da batirin mota

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

 

Advertisement

Matashin mai suna Malik Muhammad Kumo, ɗan asalin jihar Gombe ya zabi samar da injin bayin ne domin hucewa al’ummar yankunan karkara takaicin tsadar man fetur da kuma tsadar inji mai amfani da hasken rana.

Wikki Times ta ruwaito cewa Malik Muhammad dai ya hada irin wannan inji da ke samar da ruwa ta hanyar amfani da batirin mota da wasu injuna da koyel, inji yana tashi da key kamar yadda ake tada mota, yana diri yana chajin batir har lokacin da ka gaji ka kashe shi, yana awa a shirin da huɗu bai mutu ba, a jikin sa harda wajen saka chaji na waya.

Advertisement

Shekarau Ya Buƙaci Abba Da Gawuna Su Amince Da Hukuncin Da Kotun Ƙoli Za Ta Sanar

Wannan mataki nasa ya sa mutane da dama a yankunan karkara sha’awar noman rani, wanda ya zama sana’a a wajen mutane.

A cewar Malik Muhammad Kumo, abun alfahari ne a gare shi, wanda hakan wata babbar nasara ce da yake alfahari da ita ta sanadin mahaifinsa.

Advertisement

Sai dai duk da cewa wannan matashin ya ce ya samu nasarori masu yawa a baya a irin wannan fannin kirkire-kirkire, sai dai kuma akwai tarin kalubale da yake fuskanta musamman rashin kuɗi, wanda yasa ya share tsawon wata uku yana fama wajen ganin ya haɗa wannan injin a cewar sa.

Daga karshe dai yayi kira ga matasa da su yi amfani da basirar da suke da ita wajen dogoro da kansu ba tare da sai gomnati ta basu aiki ba.

Advertisement

A wani labarin kuma Shekarau Ya Buƙaci Abba Da Gawuna Su Amince Da Hukuncin Da Kotun Ƙoli Za Ta Sanar

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending