Connect with us

News

Hukumomi na cigaba da shawartar gwamna Abba Kabir Yusuf kan rushe masarautun Kano

Published

on

Gwamnan Jahar Kano alhaji abba Kabir Yusuf

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Wata kungiya mai suna Rakibu Rakibu ta al’ummar Rano-Kibiya-Bunkure, ta roki Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya yi watsi da duk wani yunkuri na rusa masarautu biyar da aka kafa a jihar.

A tuna cewa gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ta ƙara masarautu hudu da suka hada da Rano, Karaye, Bichi da Gaya, baya ga masarautar Kano.

Advertisement

Da ya ke zantawa da manema labarai a Kano, shugaban kungiyar Wali Ado Rano, ya yi ikirarin cewa dorewar wadannan masarautu buƙata ce ta mafi yawan al’ummar Kano.

Ya ce: “Ya kamata mu bayyana cewa, dorewar wadannan masarautun buƙata ce ta mafi yawan yankunan mu.

Advertisement

“Na biyu, dorewar masarautun ba wai yana nufin jefa Kano a wani hali ba kamar yadda masu adawa da hakan su ka fahimta; don haka ƴan uwanmu za su ci gaba da wanzuwa a tsakanin al’ummar Masarautar da aka dawo da su da na Masarautar Kano.”

Mista Rano ya yi nuni da cewa, daukaka darajar sarakunan gargajiya ba wani sabon abu ba ne a Najeriya, inda ya ce kara girman hakimai zuwa gundumomi ko gundumomi ga sarakuna ya kasance wani hakki ne da ake ci gaba da yi tun daga Jihadin Fulani har zuwa yau.

Advertisement

“Bai kamata a yi wa ƙarin masarautun nan wata mummunar fahimta ta siyasa ba. a cewar sa

Don haka Rano ya bukaci jama’a da su kara himma wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending