News
Gwamnatin tarayya ta bukaci hukumar ‘yan sandan kasa da kasa ta INTERPOL ta sanya idanu akan wasu ‘yan najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin tarayya ta bukaci hukumar ‘yan sandan kasa da kasa ta INTERPOL ta sanya idanu akan wasu ‘yan najeriya uku akan zargin yin takardun bogi.
Majiyoyi sun bayyana cewar ana neman wadanda ake zargin-wani jami’in babban bankin Najeriya, Odoh Ocheme da wasu mutane biyu ruwa a jallo ne akan zargin kwaikwayar sa hannun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari domin satar fiye da dala milyan 6 da dubu 200 daga babban bankin.
Hukumomi na cigaba da shawartar gwamna Abba Kabir Yusuf kan rushe masarautun Kano
Ana zargin Ocheme da kitsa almundahanar tare da yin takardun bogi da sunan Shugaba Buhari domin wawure fiye da dalar amurka milyan 6 da dubu 200 daga asusun babban bankin Najeriya, tare da Adamu Abubakar da Imam Abubakar.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mukaddashin Kwamishinan ‘Yan Sanda kuma Shugaban Sashen Kula da Ayyuka da bincike na musamman a rundunar ‘yan sandan Najeriya, Oloho Okpoziakpo
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
