Connect with us

News

Hanyoyin da za a kiyaye don kare kai da iyali daga kamuwa da Sankarau

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Sankarau cuta ce da kwayoyin suka hada da ‘Bacteria, Virus da Parasite’ ke haddasa cutar a jikin mutum.

Mutane musamman yara kanana na yawan kamuwa da cutar a duk lokacin da yanayi ya canza zuwa lokacin zafi.

VOA Hausa zatayi kawance da American university domin bunkasa yaran Hausa a fadin duniya duniya

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta bayyana cewa daga shekarar 2022 zuwa 2023 mutum 303 sun kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 190 a jihohi 29 da Babban Birnin Tarayya Abuja.

NCDC ta kuma ce duk jihohi 19 dake yankin Arewacin Najeriya da jihohin Bayelsa, Cross River, Delta, Ekiti, Ogun, Ondo da Osun dake kudancin kasar nan na daga cikin bangarorin kasar da suka fi yawan fama da bullowar cutar.

Premium Times ta ruwaito cewa bana dai Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen cewa bana jihohin Sokoto, Jigawa, Yobe da Borno na daga cikin jihohin da ka iya samun barkewar cutar saboda canjin yanayi na zafi da za su rika samu.

Advertisement

Sannan cutar ka iya bullowa a jihohin Zamfara, Kano, Bauchi, Kebbi, Katsina da Gombe saboda matsakaicin zafin da za a yi fama da shi.

Alamun kamuwa da Sankarau

 

1 Za ka ga yaro yana ta suma idan ya kamu da cutar.

 

2. Yawan kwanciya da gajiya

Advertisement

 

3. Yawan yin Amai

 

4. Cutar na kawo amai.

 

5. Curar na kawo zafin jiki wanda daga baya yakan iya zama Zazzabi.

Advertisement

 

6. Mutum zai dinga ganin jiri

 

7. Sankarewan wuya.

 

8. Rashin son ganin haske.

Advertisement

 

Hanyoyin gujewa kamuwa da Sankarau

 

1. Yin allurar rigakafi.

 

2. Tsaftace muhalli.

Advertisement

 

3. Rage cinkoso a wuri daya.

 

4. Abude tagogi domin samun isasshen iska a dakunan da ake zama.

 

5. A daina ganin cutar Sankarau a matsayin wani tsafi ne ko jifa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending