Connect with us

News

Shugaba Tinubu ya hori Attajiri su waiwayi talakawa a wannan lokaci na Azumin Ramadan

Published

on

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Shugaban kasa Bola Tinubu ya kwaɗaitar da attajirai da su waiwayi musamman talakawa da marasa galihu a wannan lokaci na azumin Ramadan domin rage wahalhalun tsananin rashi da suke fama da.

Tinubu ya fadi haka ne a wurin kaddamar da rabawa talakawa buhunan shinkafa masu nauyin Kilogiram 50kg wanda wani attajiri masoyin shugaba Tinubu, Abdullahi Yari ya yi a madadain shugaban kasan a garin Kano.

Ku yi wa ma’aikata ƙarin albashi don ba su walwala —Ƙungiyar Ƙwadago NLC

Mai taimakawa shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai Abdulaziz Abdulaziz ya wakilce shi a wurin taron.

Tinubu ya yaba da wannan hubbasa da Yari ya yi domin talakawa.

Attajiri Yari ya samar da manyan motoci 140 cike da buhunan shinkafa masu nauyin kilogiram 50.

Advertisement

Tinubu ya yi kira ga ƴanNajeriya da su yi amfani da wannan wata domin yin addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaban kasa.

” Duk duniya an amince cewa shugabanci ba aikin mutum ɗaya bane, saboda haka dole masu abin hannu su rika waiwayen talakawa da marasa ƙarfi don a rika taimaka musu.

” Mu zo gaba ɗayanmu, mu haɗe wuri guda mu dunƙule, domin cigaban kasar mu.

Abubakar Danburam wanda ya wakilci Yari a wurin taron ya ce kowace babbar mota na dauke da buhunan shinkafa 84,000 masu nauyin 50kg.

Ya ƙara da cewa za a raba shinkafar ga akalla gidaje 500,000 a yankin Arewa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending