Connect with us

News

An tsinci gawar wani mutum da ba a san kowane ne ba yashe a kan titi a birnin Kano.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

An tsinci gawar wani mutum da ba a san kowane ne ba yashe a kan titi a birnin Kano.

An tsinci mutumin a kan titin zuwa gidan gwamnatin jihar a ranar Litinin.

Shugaba Tinubu ya hori Attajiri su waiwayi talakawa a wannan lokaci na Azumin Ramadan

A cewar wasu mutane da ke kusa da wajen da aka tsince gawar, suna zargin wasu bata-gari ne suka makure wuyansa da wayar lantarki har sai dai suka tabbatar ya daina numfashi.

Aminiya ta ruwaito cewa an garzaya da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase domin ba shi agajin gaggawa.

Kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending