Connect with us

News

Tallafi Ga Marasa Lafiya: Mun San Cewa Wannan Mafari Ne A Wajan Mai Girma Gwamna —DR Nagoda 

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Sakataren zartarwa na hukumar kula da asibitocin jihar Kano Dr Mansur Mudi Nagoda ya bayyana godiyarsa ga gwamnan jihar Kano Alh Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake tada hankali ga duk majinyatan da ke kwance a asibitocin jihar Kano.

A wajen rufe rabon da aka yi a babban asibitin Dambatta wanda shi ne wuri na karshe da suka karbi  shinkafa da masara mai nauyin kilogiram 10.

An tsinci gawar wani mutum da ba a san kowane ne ba yashe a kan titi a birnin Kano.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da jami ar yada labarai ta hukumar kula da asibitocin jihar Kano Samira Suleiman ta turawa da Jaridar Inda Ranka 

Sanarwar ta kara da cewa Dakta Nagoda ya bayyana cewa, an ba da tallafin ne ga majinyatan da ke kwance a kowane gida domin fara azumin watan Ramadan. .

“Muna so a madadin Hukumar Kula da Asibitoci na gode wa Mai Girma Gwamna da wannan gagarumin tallafi, mun san cewa wannan mafari ne kamar yadda ka kuma mika wa kananan ma’aikatan hukumar wannan karimcin,” inji shi.

Advertisement

Daga karshe ya yabawa gwamnan jihar bisa baiwa hukumar kula da asibitocin jihar Kano kuma a shirye yake ya bada goyon baya ta ko wanne hali ya kara da cewa alkawarin da ya dauka na farfado da harkar lafiya a kano yana nan daram.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending