Opinion
Finafinan Daba Da Akeyi Su Na Matukar Taka Rawa Wajen Jefa Yaran Mu A Harkokin Daba —Dandago

Yakamata Gwamnati ta magantu akan matsalar Daba da ta addabi alummar mu da Kuma yara kanana Wanda kamata ye ace yaran gabaki dayan su su na makaranta ko kuma wani waje na koyan Sana,a domin su samawa kansu kudin taro da sisi.
Mun yi duba da yadda matsalar Daba ta yara kanana take kara ta,azzara a garin Kano Wanda kuma babu ta inda yaran nan su ke koyan fadace fadcen ne face kallace kallacen Finafinan Hausa wadanda su ka Shafi harkar Daba da dade sauran su.
Duba da wannan Babbar matsalar da a ka gano mu ke mika kokon barar mu ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Eng Abba Kabir Yusif da yayi bincike a kan wannan nazarin na mu Domin a dakatar da ireren wadannan Finafinan domin ceto rayuwa Alummar mutanan Jihar Kano.
Daga Comr. Fatihu Adam Abubakar (Dandago)