Opinion
Jaridar Inda Ranka ta taya Mubarak auwal unguwa uku murnar jika shekaru 25
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kamfanin YAKAM MULTIMEDIA masu buga Jaridar Inda Ranka ta taya matashin Dan jarida Mubarak auwal unguwa uku murnar cika shekaru 25 a duniya
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Shugaban kamfanin Kabiru Basiru Fulatan ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a Jahar Kano
Sanarwar tace Mubarak ya kasance dan jaridar dake aiki da kafar yada labarai ta vision FM Kano a matsayain mataimaki ga Shugaban sashin siyasa haka zalika yakesan cigaban Yan uwan,sa matasan Yan jaridar dake tasowa Kuma yake aiki dasu ba tare da nunamusu wariya ko Kuma tsangwamaba yayin gudanar da aikin,su ba
Shugaban indaranka yace Hakika yaban gwani ya Zama dole Kuma Abu ne a zahiri ganin Yadda Mubarak ke baiwa jaridar inda ranka gudun mawa tun lokacin da kafar ke neman Yadda za,a bunkasa Al,amuran,ta
Hakika nasan da cewa bawai iya jaridar inda ranka wannan matashin dan jaridar ya baiwa gudunmawa ba harda wasuma da dama.
Mubarak unguwa ya fara da aiki tun daga matakin Mai kawo rahotanni wato (reporter) kafin ya Zama Mai karanto labarai (newscaster) kafin daga bisani ya zanto Mai sharhi da Kuma Mai shirya Shirin siyasa
A madadin daukacin ma, aikatan jaridar inda ranka munaiwa Mubarak auwal unguwa uku murnar cika shekaru 25 tare da fatan Allah ya inganta rayuwar,sa da Kuma fatan samun nasarori masu yawa a fadin rayuwar,sa